OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rushewar Gini: Yara Uku Sun Rasu A Jigawa

Rushewar Gini: Yara Uku Sun Rasu A Jigawa

Yara 3 sun rasu bayan wani gini ya faɗa kan su a kauyen Jigawar Tsada da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

Shugaban al’ummar yankin ya tabbatar da faruwar iftila'in wanda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.

 A cewar sa, yaran suna barci ne a lokacin da ginin ya ruguje, Wanda yayi sanadiyar mutuwar su nan take.

Da yake zantawa da jaridar Daily Post, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu Adam shi ma ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce an kwashe sa’o’i da yawa ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Yaran da suka rasu dukkansu ‘yan mata ne kuma an bayyana sunayensu kamar haka Farida Idi (6), Mariya Idi (3), da Bilkisu Yahaya mai shekara 1 da wata 6.

Dsp Lawan Shiisu ya bayyana cewa a lokacin da labarin rugujewar ya iso gare su, jami’an tsaro sun je wurin, inda suka kwashe gawarwakinsu aka garzaya da su babban asibitin Dutse.

 A cewarsa, dukkan ‘yan matan uku likita ne ya tabbatar da mutuwarsu, kuma an mika gawarwakinsu ga iyayansu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

 Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyayansu yana mai addu’ar Allah ya basu ikon jure wannan rashi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci