OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar Sojin Najeriya Ta Amince Da Ajiye Aikin Sojoji 300

Rundunar Sojin Najeriya Ta Amince Da Ajiye Aikin Sojoji 300

Sojoji dari biyu da arba'in da uku (243) ne zasu ajiye  aiki bisa dalilai na rashin lafiya da buƙatu na kashin kai.

Wani rahoto da jaridar Punch ta fitar ya ce, sojojin za su yi adabo da aikin sojin aga ranar sha biyar (15) ga watan Janairu na shekara 2023. In da a ranar 15 ga watan Fabarairu na shekarar kuma za su bar aiki a hukuman ce.

Rahoton ya ƙara da cewa, an gano bukatar ajiye aikin sojojin ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 15 ga watan Agusta, inda aka umarce su da mika bayanan su don tantancewa a ranar 15 ga watan Oktuban wannan shekara, tare da damka makamai da sauran kayan aiki da suke amfani dashi a ga rundunar. 

Mai magana da yawun rundunar soji ta kasa, Brigediya Janar Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da barin aikin jami'an rundunar, inda ya kara da cewa, shugaban rundunar sojin ƙasar nan, Umar Faruk ya amince da hakan.

Onyema ya kara da cewa, daga cikin dakarun da za su ajiye aiki, akwai Warrant ofisa guda daya da sauran jami'ai 242. 

 

 

SOB

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci