OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rikici: Shugaban jam'iyyar APC ya zargi Tinubu da saba alkawari a kan kwamitin yakin neman zabe

Rikici: Shugaban jam'iyyar APC ya zargi Tinubu da saba alkaw

Shugaban jam’iyyar APC, Abdulahi Adamu, ya zargi Bola Tinubu da yin watsi da yarjejeniyar da akayi akan kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa (PCC).

Mista Adamu, a cikin wata wasika da ya aike wa Mista Tinubu, ya zargi Tinubu da yin watsi da kwamitin ayyuka na jam’iyyar.

Wannan itace sabuwar rikicin data kunno kai a cikin jam'iyyar game da 'yan kwamitin yakin neman zabe.

Jaridar Allnews ta ruwaito yadda gwamnoni suka yi barazanar yin zagon kasa ga yakin neman zaben shugaban kasa kan sunayen da aka fitar.

Rashin amincewar gwamnonin shi ya tilasta aka dage ranar taron kaddamar da 'yan kwamitin har zuwa nan da wani lokaci.

Ko da yake, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dage dokar data saka na hana yakin neman zabe a ranar Laraba, sai dai har yanzu jam'iyya mai mulki ba ta fara yakin neman zaben ta ba, kasancewar Mista Tinubu baya kasar.

Mista Adamu, a cikin wasikar da aka fitar,ya ce kwamitin ayyuka na jam'iyyar ta yi nadamar samun wannan labari.

Inda ya kara da cewa Tinubu ya yi alkawarin haɗa kai da kwamitin ayyuka na jam'iyyar.

Duk da cewa Tinubu da Adamu sun karyata rade-radin cewa akwai baraka a baya, amma akwai rahotannin cewa akwai 'yar tsama tsakanin su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci