OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Ribadu ya karbi bakuncin daliban jami'ar zamfara da ma'aikatan da aka ceto

Ribadu ya karbi bakuncin daliban jami'ar zamfara da ma'aikat

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya karbi bakuncin dalibai da ma’aikatan jami’ar tarayya da ke Gusau su 22 da aka yi garkuwa da su, wadanda aka ceto a ranar Lahadi. 

 

Mutane 22 da suka hada da dalibai 15 da ma’aikatan jami’ar bakwai, an sace su ne daga jami’ar a watan Satumban 2023. 

 

Ribadu ya ce cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, NCTC ce ta dauki nauyin aikin ceton ranar Lahadi. 

 

Yayin da yake karbar wadanda aka ceto a ranar Litinin a Abuja ya hore su da su zama masu karfafa zuciyoyin su, kada su bari wannan lamarin ya kassara su.

Ya Kuma yi godiya ga iyayen daliban bisa juriyar da suka nuna a lokacin da ake kokarin ceto su, hadi da jinjinawa jami'an tsaro bisa fafutukar da suke na ganin an kawo karshen matsalar tsaro a kasarnan.

 

 “A madadin shugaban kasa, ina godiya ga duk wadanda suka tallafa wajen ceto wadanda akayi garkuwa dasu ba tare da an rasa rai ko biyan kudin fansa ba. Hakan babbar nasara ce a kokarinmu na ceto duk wadanda aka yi garkuwa dasu a kasarnan " a cewar Ribado

 

 "Ya zuwa yanzu munyi nasarar ceto mutane sama da dubu ba tare da an kai ruwa rana ba. Wannan karon shi ne mataki na karshe a cikin jerin ayyukan ceto da muka yi a 'yan watannin da suka gabata don ceto wadanda aka yi garkuwa da su a baya-bayan nan". In ji Shi.

 

Ribado ya tabbatar da zasu cigaba da ƙarfafa jami'an tsaro hadi da daukar matakan tsaro don kawo karshen sace-sacen al'umma.

 

 Tun da fari, kodinetan hukumar NCTC, Manjo Janar Adamu Laka, ya rawaito cewa an sace wadanda aka ceto daga makarantar ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2023, da misalin karfe 2:30 na safe, lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai hari a gidajen kwanan dalibai uku a unguwar Sabon Gida dake Gusau.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci