OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rashin Tsaro: Gwamnatin Oyo Ta Aike Da Jami'an Tsaro Zuwa Yankin Ipapo/Iseyin

Rashin Tsaro: Gwamnatin Oyo Ta Aike Da Jami'an Tsaro Zuwa Ya

Gwamnatin jihar Oyo ta tura tawagar jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a yankin Ipapo/Iseyin a gundumar Oyo ta Arewa.

Lamarin ya faru ne bayan sace wasu manoma da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a ranar Asabar.

Gwamnatin jihar ta kuma yi kira ga al’ummar Ipapo da su kwantar da hankalinsu dangane da sace mutane hudu da aka yi.

Adeniyi Adebisi, kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar a wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa an aike da tawagar jami’an tsaro da suka hada da jami’an ‘yan sanda da sojoji domin tallafawa zaman lafiyan yankin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar, Wasiu Olatunbosun, ta bada tabbacin cewa gwamnati za ta dauki kowane mataki don ganin an dawo da wadanda aka sace zuwa ga ‘yan uwansu cikin koshin lafiya.

Ya bayyana cewa duk da faruwar wannan mummunan lamarin a yankin Ipapo/Iseyin, gwamnatin jihar Oyo ta na kokarin kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar,da ,manoma.

“Tawagar sojojin ba wai kawai ceto wadanda abin ya shafa ba kawai za su yi ba har ma da tabbatar da daukar matakin da ya dace kan wadanda suka aikata wannan aika-aika.

“A bisa haka ne aka tattaro dukkan jami’an tsaro a jihar da suka hada da sojojin Najeriya zuwa yankin domin ganin an bankado masu laifin.

“Gwamnatin jihar ta hada kai da jami’an tsaro domin kubutar da wadanda aka sace ba tare da bata lokaci ba.” inji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci