OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Rundunar Yan sandan Katsina ta kama masu fashi da makami 22

Rundunar Yan sandan Katsina ta kama masu fashi da makami 22

The Police said the arrest was possible through credible Intel

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutane 22 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da kuma mutane 36 da ake zargi da aikata laifukan fyade da luwadi a jihar a cikin watan Afrilu. 

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan nasarorin da rundunar ta samu a cikin watan Afrilu.

 

 Sadiq-Aliyu ya bayyana cewa an kama mutane goma da ake zargi da kisan kai a wannan lokaci. A cewarsa, an samu manyan laifuka guda 81 da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai, da satar dabbobi. 

 

“A cikin wannan lokaci, an gurfanar da wasu kararraki 69 a gaban kotu, yayin da daga cikin adadin mutane 145 da ake zargi da hannu a wadannan laifuka an kama mutane 58.

 

 “Hakazalika, rundunar ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga 12, ta ceto sama da mutane 30 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato dabbobi 492 da aka sace,” in ji Sadiq-Aliyu. 

 

 PPRO din ya kuma bayyana cewa, a ranar 5 ga watan Mayu, rundunar ta samu nasarar dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wasu motocin kasuwanci guda biyu a Unguwar Boka hamlet, dake kan titin Funtua-Gusau, tare da ceto mutane 52. 

 

 Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kaiwa motocin harin ba zata lamarin da ya tilasta wa direban ya karkata daga kan titin zuwa dazuzzukan da ke kewaye. 

 

“Bayan samun rahoton, nan take DPO ya tattaro jami’an tsaro tare da kai daukin gaggawa, inda suka yi artabu da maharan da muggan makamai, inda suka yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da fasinjojin tare da kubutar da dukkan fasinjojin ba tare da samun rauni ba. Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci