OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

PDP A Gombe Ta Gargaɗi Tsohon Ministan Ƴan Sanda Kan Maƙarƙashiya Wa Jam'iyar 

PDP A Gombe Ta Gargaɗi Tsohon Ministan Ƴan Sanda Kan Maƙa

Jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe ta gargaɗi tsohon ministan harkokin ƴan sanda, Adamu Waziri, bisa zarginsa da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan zargin da ake masa na ɗaukar nauyin wata zanga-zangar nuna adawa da tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo.

Jam’iyyar ta sake tabbatar da biyayyar ta ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaben 2023 mai gabatowa, Atiku Abubakar, tare da bayyana shugabancin Dankwambo.

A cewar sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PDP na jihar Gombe, Murtala Usman, yayin da yake mayar da martani kan zanga-zangar da wasu matasa da ake zargin Waziri ne ya dauki nauyi.

Sanarwar a ranar Lahadi ta ce waɗanda suka mamaye sakatariyar jam’iyyar ta jihar suna zanga-zangar nuna adawa da Ibrahim Dankwambo, ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa.

 “A yau ne wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP daga jihar Yobe suka mamaye ofishin jam’iyyar PDP domin shafawa shugaban jam’iyyar mu Ibrahim Hassan Dankwambo (Talban Gombe) bakin jini da haddasa rashin jituwa da hargitsi.

“Wanda ya ɗauki nauyin ya tsaya takara sau da yawa a jihar Yobe kuma bai iya lashe ko daya ba, sanannen karuwan siyasa ne kuma dan kasuwan siyasa.

"Ya kamata ya je ya damu da rikicin siyasar da ke addabar jihar Yobe, ya daina tsoma baki cikin harkokin siyasar jihar Gombe, cewar Jaridar Punch.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci