OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Osinbajo Ya Biya Naira Miliyan Dari Kudin Fom Din Takarar Shugaban Kasa

Osinbajo Ya Biya Naira Miliyan Dari Kudin Fom Din Takarar Sh

Mataimakin shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya biya Naira miliyan dari na fom din takarar sa na shugaban kasa a 2023 karkashin jam'iyyar APC.

Sanata Kabiru Gaya ne ya karbi fom din a madadin mataimakin shugaban kasan a ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa Gaya na daya daga cikin shugabannin kungiyar yakin neman zaben Osinbajo.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a watan da ta gabata.

Bayan nuna sha’awar sa, mataimakin shugaban kasar ya dade yana zagayawa kasar domin tattaunawa da wakilan jam’iyyar APC mai mulki.

Ku tuna cewa jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben fidda gwani a karshen watan nan bayan da aka tsawaita sayar da fom na kwanaki hudu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci