OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

NSCDC ta Cafke Mutane 11 da Ake Zargi da Fashin Daji a Sokoto

NSCDC ta Cafke Mutane 11 da Ake Zargi da Fashin Daji a Sokot

Hoto Daga: Infoguide Nigeria

 

Hukumar tsaro ta Civil Defence dake Jihar Sakkwato ta cafke mutane 11 da ake zargi da fashin daji a jihar.

 

Kwamandan rundunar ta NSCDC a Sakkwato, Mista Muhammad Dada ne ya tabbatar da faruwan lamarin a jiya lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi a Sokoto.

 

Dada ya ce an cafke wadanda ake zargin ne tare da wata kungiyar ‘yan banga na karamar hukumar Wurno dake jihar.

 

A cewar sa, “Wannan ci gaban ya kai mu ga cafke wasu mutane bakwai da ake zargin barayin shanu ne da aka gano suna cikin tawagar‘ yan bindiga da ke addabar Tureta, Dange/Shuni da Rabah na jihar.

 

“Daga cikin wadanda ake zargi akwai Alti Shehu mai shekaru 25, wanda wasu shekarun baya hukumar ta kama shi, ta gurfanar da shi a gaban kotu sannan aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

 

“Yayin da sauran su ne Buba Bello, Abdullahi Hassan, Sani Duna, Abu Gidado, Shehu Modibo da Ibrahim Modi.

 

“An kwato shanu arba’in da hudu da aka sace daga hannun wadanda ake zargin kuma a halin yanzu suna tsare a karamar hukumar Wurno."

 

Kwamandan ya ci gaba da cewa rundunar ta samu nasarar cafke Muhammadu Aminu da Buba Garba, wadanda suka furta cewa suna da hannu a ayyukan garkuwa da mutane a jihar.

 

Kwamandan ya kara da cewa, “Sun yarda a cikin bayanan su na ikirarin cewa suna da hannu cikin jerin garkuwa da mutane da kashe marasa laifi.

 

“Abin takaici cikin duka batun shine bayan duk aika-aikan da sukayi, ana ba su alawus na N10,000 kacal."

 

Dada ya ce jami’an rundunar sun kuma kama Umar Sanda da Nura Bello, wadanda ake zargin masu kai wa ‘yan fashin bayanai ne da samar musu abinci.

 

Kwamandan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda ake zargin kuma a karshe za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci