OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Abokan Tambuwal Sun Saya Masa Fom Din Takarar Shugaban Kasa Na N40m a PDP

Abokan Tambuwal Sun Saya Masa Fom Din Takarar Shugaban Kasa

Governor Aminu Waziri Tambuwal| Photo Source: PremiumTimes

Abokan gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal sun ba shi kyautar fom din miliyan 40 na takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a karkashin jam'iyyar PDP.

Kungiyar abokan ta kasance karkashin jagorancin babban lauya Aree Olumiyiwa Akinboro (SAN).

Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Hon. Bature ya ce an bi tsarin da ya dace wajen samun fom din.

Jagoran abokan, Aree Olumiyiwa Akinboro (SAN) ya bayyana cewa kungiyar ta kunshi ‘yan Najeriya masu kishin kasa wadanda suke ganin Tambuwal ne kadai zai hada kan kasar.

Ya kara da cewa kasar na cikin halin damuwa da ke bukatar hannun Tambuwal.

Yayin da suke lura cewa abotarsu ta kai shekaru 30, yace imaninsu gare shi ba ya girgiza.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Yana da kamun kai da hankali, mutane suna tambaya ko yana da kudin da zai cika wannan buri, shi ya sa muka zo nan don mu saya masa wannan fom, bai sani ba amma mu a matsayinmu na kwararu ba 'yan siyasa ba, muna son shi da jagoranci."

Ya kuma kara da cewa, batun yanki ya kamata ya zo ne kawai bayan jam’iyyar PDP ta gabatar da mafi kyawun dan takararta.

Akinboro ya kara da cewa Tambuwal ne kadai mai zuciyar kowane dan Najeriya ba tare da la’akari da kabila ba.

"Kalle mu kawai, muna da Yarabawa, Igbo, Ibibio, kuma muna cewa, PDP, ku sa kafarku da tafi kyau gaba," in ji shi.

Ya kuma kara da cewa kungiyar ta yi imanin cewa PDP ce ke da mafi kyawun damar lashe zaben shugaban kasa a 2023 matukar an gabatar da Tambuwal a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) ta sanar da bude siyar da fom din tsayawa takara da kuma nuna sha'awar tsayawa kuma tuni ta fara samun masu saye.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci