OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Jiga-Jigan Gwamnatin Jihar Sokoto Sama da Goma Sun Ajiye Aiki

Jiga-Jigan Gwamnatin Jihar Sokoto Sama da Goma Sun Ajiye Aik

Sokoto State Governor, Aminu Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya amince da takardar ajiye aikin mataimakin sa, Hon. Manir Muhammad Dan Iya da sauran su.

Gwamnan ya kuma amince da ajiye aikin kwamishinonin sa guda 10 da sakataren gwamnatin jihar da kuma shugaban ma’aikatan sa.

Mataimakin gwamnan ya kuma kasance mai kula da ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar Sokoto.

Sauran jiga-jigan gwamnatin da suka ajiye aiki sun hada da Sakataren Gwamnatin, Mallam Sa’idu Umar da shugaban ma’aikatan gwamnatin Mukhtar Umar Magori.

Kwamishinoni goma da suka yi murabus sun hada da na ma’aikatun kudi, muhalli, matasa da wasanni, filaye da gidaje, da sana’o’i da tsaro.

Sauran su ne Hon. Bashir Gidado na ma'aikatar kasuwanci, Salihu Maidaji na ayyuka, Shu'aibu Gwandu Gobir na albarkatun ruwa, Abubakar Maikudi Ahmad na ma'adanai da kuma Abdullahi Maigwandu na harkokin addini.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci