OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Sakkwato Ta Hana Saka Hotunan Yaƙin Neman Zabe a Wuraren Jama'a

Gwamnatin Sakkwato Ta Hana Saka Hotunan Yaƙin Neman Zabe a

minu Waziri Tambuwal

Gwamnatin jihar Sakkwato ta haramta sanya hotunan yakin neman zabe a wuraren taruwar jama'a.

Mataimaki na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, wanda ke kula da hukumar raya birane da yankuna na jihar, Sidi Aliyu Lamido ne ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da jam’iyyun siyasa a jihar a ranar Alhamis.

Lamido, wanda ya yi Allah wadai da sanya allunan yakin neman zabe a kan shataletale, masallatai da katangar coci-coci, ya bayyana irin wannan a matsayin karya doka.

Ya bukaci ‘yan siyasa da su hakura da wannan aiki ko kuma su fuskanci fushin doka.

“Ba za mu iya barin wannan ta’addanci ta ci gaba da gudana ba saboda baya ga karya dokar mu, hakan kuma ya saba wa dokar zabe saboda bai kai lokacin yakin zabe ba,” in ji shi.

Lamido ya bayyana cewa akwai hanyar sanya fosta a jihar, cewar Jaridar Daily Trust.

“Kafin ka sanya fosta a jihar dole ne ka rubuta mana, neman izini.  Dole ne ku gaya mana inda kuke son sanya hotunanku.  

"Idan yana da kyau a gare mu, mun yarda.  Idan ba haka ba, mu gaya muku inda za ku sanya su,” inji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci