OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jonah Jang Ya Zargi Ayu, Tambuwal Da Maƙarƙashiya Wajen Hana Wike Takarar Shugaban Ƙasa A PDP

Jonah Jang Ya Zargi Ayu, Tambuwal Da Maƙarƙashiya Wajen Ha

Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya yi zargin cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi wani shiri na sirri tare da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, don tauye neman takarar Gwamna Nyesom Wike da sauran 'yan takara a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar.

Jang, wanda ke da alaka da  Wike, ya bayyana haka ne a ranar Larabar nan jin kadan bayan gudanar da wani taron ‘ya’yan jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Gwamna Wike a garin Fatakwal.

Gidan talabijin na Channels sune suka sake BidiyonJang a yayin furucin wannan maganar a shafin su na Facebook.

Tambuwal,wanda ya kasance tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta PDP wanda a yanzu kuma shine babban darakta na kwamitin yakin neman zaben Atiku.

Saura 'yan awanni gabannin gudanar da zaben fidda gwamma Mista Tambuwal ya janye wa Atiku kuma ya bukaci magoya bayansa da su mara masa baya, Sakamakon janyewar da Tambuwal ya yi wa Atiku, hakan ne ta sa ya doke Gwamna Wike da sauran masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Sa'o'i kadan bayan kammala taron zaben fidda gwani, an hangi Ayu a cikin wani faifan bidiyo ya ziyarci gwamnan Tambuwal a gidansa da ke Abuja, inda ake zargin cewa yaje ne domin ya masa godiyar janyewa Atiku.

Hakan na kunshe ne a cikin faifan bidiyo da ya bayyana. “Na gode, na gode. Kai ne gwarzon taron,” Mista Ayu ya bayyana haka ga Tambuwal Da yake magana bayan taron kungiyar da Wike ke jagoranta a Fatakwal, Mista Jang ya bayyana Mista Ayu a matsayin “alkalin wasa” wanda ya taimaka wa daya daga cikin 'yan takara doke sauran abokan hamayya.

“Zuwan Mista Ayu, gidan Tambuwal ya je yana yabonsa yana masa kirari yana kiransa gwarzon taron, hakan ya nuna cewa akwai wani shiri na sirri da ya gudana tsakanin shi da Tambuwal don rage wa sauran ’yan takara karfin ciki har da Gwamna Nyesom Wike.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci