OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Najeriya Na Kashe Dala Miliyan 100 A Ciyar Da  Ƴan Makaranta Miliyan 10 - Gwamnati

Najeriya Na Kashe Dala Miliyan 100 A Ciyar Da  Ƴan Makaran

Chris Ngige

Gwamnatin tarayya ta ce tana kashe kimanin dala miliyan 100 wajen ciyar da yara miliyan 10 na Najeriya a karkashin shirin ciyar da makarantu na ƙasa.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Sanata Chris Ngige ne ya bayyana haka a ofishin sa a lokacin da ya karbi bakuncin jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard.

Mista Ngige ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta ɓullo da shirin ciyar da dalibai a karkashin shirinta na tsaro, domin janyo hankalin yaran da ke gararamba zuwa makaranta.

Ya ce gwamnatin ta kuma ɓullo da tsare-tsare na kare al’umma don yaki da talauci, wanda shi ne babban abin da ke haifar da yawaitar sa yara aikin wahala da azaba.

Sanarwar wanda Olajide Oshundun, shugaban yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ya fitar ta ruwaito Ngige na cewa, “Mun ɓullo da shirin ciyar da makarantu na ƙasa a karkashin tsarin zamantakewar mu, domin jawo yaran su koma makaranta.  

"Ya zuwa yau, muna ciyar da yara miliyan 10 a fadin ƙasar nan.

"Mun kashe kusan dala miliyan 10 akan wannan, cewar Jaridar Vanguard.

 “Mun kuma ɗauki ƙarin makarantu zuwa yankunan da ke fama da ayyukan da azabtar da yara don sanya ilimi kyauta.

Daɗin daɗawa da kuma  dokar ba da ilimi ta bai daya kuma kyauta a faɗin ƙasar, sa'annan da dokar kare hakkin yara.

“Ga nakasassu kuwa, mun ɓullo da hukumar kula da nakasassu domin ba su cikakken tallafi don kada su ji cewa suna da nakasa."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci