OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zaben 2023: Idahosa Ya Bada Tabbacin Cancantar Kwankwaso

Zaben 2023: Idahosa Ya Bada Tabbacin Cancantar Kwankwaso

​​​​​​Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Bishop Idahosa, ya bayyana cancantar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Idahosa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja gabanin babban zabe na 2023. 

Ya bayyana cewa tikitin Kwankwaso/Idahosa ya fi dacewa wajen gyara kalubalen da ke addabar kasar, ya kuma kara da cewa zai magance matsalar ababen more rayuwa da kuma kula da albarkatun kasa.

Ya ce shugaban nasa "Yana da tsayin daka a fafatawar da za a yi don gudanar da mulkin kasar kuma dan takarar shi ne ya fi kowa kwarewa a cikin duk masu neman kujera mafi girma a kasar."

Ya kara da cewa dan takarar jam’iyyar NNPP yana da kyakkyawan tarihi a matsayin Sanata tsakanin 2015 zuwa 2019 da kuma matsayin gwamna na wa’adi biyu daga 1999 zuwa 2003 da 2011 zuwa 2015 da kuma ministan tsaro tsakanin 2003 zuwa 2007.

Idahosa ya ce da irin wannan shaidar, Kwankwaso zai fito da kwarewa ta yadda wasu ba za su iya yin fariya ba kuma baya ga kasancewarsa kwararre mai kula da harkokin gudanarwa, “Kwankwaso kuma babban gwani ne”.

“Saboda haka, za ka iya tabbatarwa cewa a matsayin shugaban kasa, zai zage damtse tare da daukar kwararrun kwararru daga gida da waje domin juya tattalin arzikin kasar nan."

Idahosa ya ce Kwankwaso zai tabbatar da cigaban dan Adam da kuma inganta ilimi a gwamnatin sa.

Ya ce za a zuba jari mai yawa a fannin kiwon lafiya wanda zai sa Najeriya ta zama kasar da za a dinga shigowa don magani daga Kasashe. 

Idahosa ya ce za su kuma tabbatar da bin doka da oda a duk matakan gwamnati.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci