Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da ofisoshin yakin neman zabe a jihar Kebbi.
Kwankwaso ya bayyana jin dadin sa kan dimbin magoya baya da suka tarbe shi a jihar.
Dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana jin dadin sa a wata zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi.
Ya bayyana cewa shi da jam’iyyar sa a shirye suke su tunkari zaben 2023 tare da goyon bayan jama'a a kowace jiha ta kasar nan.
A cewar sa: “Mun yanke shawarar zuwa mu ga abubuwa.
"NNPP ta tsayar da 'yan takarar Majalisun Jihohi, 'Yan Majalisun Tarayya, Majalisar Dattawa da Gwamna a jihar Kebbi kuma goyon baya na da yawa da karfafa gwiwa".
Kwankwaso wanda ya yi magana kan tsare-tsaren sa a fannin ilimi a Najeriya, ya ce yana da tarihin da ‘yan Nijeriya suka shaida a fannin tun lokacin da ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas.
Ya kuma bayyana cewa ya ba da fifiko kan ilimi da samar da ababen more rayuwa a tsawon wa’adin sa na shekara takwas a matsayin gwamna.
A cewar sa, ya dauki nauyin daukar ‘yan asalin jihar da waje sama da dubu uku don yin karatu a kasashen waje a fannin likitanci da sauran fannoni.
Ya kara da cewa yana da shirin maimaita hakan a kasar idan ya ci zaben shugaban kasa a 2023.
A lokacin da yake tsokaci kan matsalar rashin tsaro a kasar, ya zargi jam’iyyar adawa ta PDP da jam’iyyar APC, inda ya kwatanta su a matsayin jam'iyya daya.
0 Tsokaci