OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane da dama sun mutu bayan taka bama-bamai a Jihar Borno

Mutane da dama sun mutu bayan taka bama-bamai a Jihar Borno

Wasu matafiya da ba a tantance adadin su ba sun mutu bayan da suka taka wasu bama-bamai a jiya a jihar Borno.

Ana zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa wadannan bama-bamai a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa zuwa Chibok.

‘Yan ta’addan sun kuma kai farmaki kauyen Njilang da ke karamar hukumar Chibok a jihar, inda suka lalata gidaje.

Mamayan da suka kai ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Vanguard, Shugaban karamar hukumar Chibok, Umar Ibrahim ya ce ya samu kira akan harin da aka kai.

A cewar sa: “Eh, na samu kiran waya a yau (jiya) cewa ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai wa daya daga cikin al’ummata, Njilang hari.

"Ko da yake har yanzu cikakkun bayanai basu bayyana ba, wasu da suka kira sun sanar da ni cewa an kashe mutane uku yayin da aka lalata kayayyakin more rayuwa."

A cewar majiyoyi, 'yan ta'addan sun yi ta harbe-harbe a kan mutanen da suke gudu domin tsira a lokacin da suke kwasar ganima a shaguna tare da lalata gidaje.

A halin yanzu dai ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba sakamakon harin. 

Ku tuna cewa gwamnatin jihar ta sake bude hanyar Maiduguri zuwa Damboa zuwa Chibok zuwa Askira/Uba kwanan nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci