OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

MURIC Ta Bukaci A Yi Adalci Kan Kisan Da Aka Yi Wa Goni Aisami

MURIC Ta Bukaci A Yi Adalci Kan Kisan Da Aka Yi Wa Goni Aisa

The late Sheikh Goni Aisami was shot twice by a man claiming to be a soldier during a lift

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci a yi adalci kan kisan da aka yi wa wani shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami na jihar Yobe.

A ranar Juma’a ne wasu sojoji biyu suka kashe Sheikh Aisami bayan ya taimakawa daya daga cikin wadanda ake zargin.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar ranar Litinin.

Akintola ya bayyana kisan a matsayin zalunci, rashin tausayi da rashin Imani. 

A cewarsa: “An kashe fitaccen malamin addinin musuluncin nan a Gashua, jihar Yobe, Shaykh Goni Aisami, a ranar Juma’a 19 ga watan Agusta, 2022 da wani soja da ya yi ikirarin yana bakin aiki ya kuma nemi a dauke shi daga Nguru zuwa garin Jajimaji.

“Yayin da muke yaba wa rundunar ‘yan sandan Yobe bisa kama wadanda ake zargin, muna kira da a gaggauta yin adalci kan wannan lamari.

“Kisan zalunci ne, rashin tausayi da rashin imani.

“Wajibi ne a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun da ke da hurumin shari’a da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike.

"Muna gargadi game da duk wani lauje cikin nadi."

Ya kuma yi nuni da irin sadaukarwar da sojojin Najeriya ke yi wajen ganin an kubutar da kasar daga masu aikata laifuka.

Ya ce: “Yayin da karfafan sojojin mu ke kwana ba barci don ‘yan Nijeriya su kwana da idanuwan su a rufe, wasu miyagu a cikin su sun rika yin fashi da kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

"Wadannan sojoji biyu, Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon na 241 Recce Battalion Nguru da suka amsa laifin su munanan misalai ne kuma dole ne doka ta dauki matakin da ya dace."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci