OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kokarin Daliban Mu Ya Tabbatar Da Ingancin Zuba Jari Na Gwamnati Akan Ilimi - Buni

Kokarin Daliban Mu Ya Tabbatar Da Ingancin Zuba Jari Na Gwam

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce dimbin jarin da gwamnatin sa ke zubawa a fannin ilimi a jihar na samun sakamako.

Ya ce kwazon da dalibai suka yi a jarabawar kammala sakandare a cikin shekaru biyu da suka wuce ya tabbatar da kokarin gwamnati.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau a Damaturu, babban birnin jihar lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga kungiyar Progressive Young Women Forum. 

Buni ya kara jaddada kudirin sa na inganta fannin ilimi.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen gyara wa da gina makarantu da dama a matsayin hanyar rage cunkoso a ajujuwa domin samar da ilimi mai inganci.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mamman Mohammed ya fitar.

A cewar sa, gwamnatin sa tana horas da malamai tare da sake horas da su domin inganta aikin.

Da yake magana kan fannin kiwon lafiya, Buni ya ce zai ci gaba da tallafa wa bangaren don inganta kiwon lafiya mai sauki ga jama’a.

Ya kara da cewa: “Daya daga cikin fannin da ke samun kulawar gwamnati shi ne samar da arziki da karfafa tattalin arziki wanda ya shafi maza da mata.

"A halin yanzu gwamnati na aiki akan wani shiri na tallafa wa matasa da aikin yi"

Ya kuma tabbatarwa da Kungiyar goyon bayan sa. 

A nata jawabin, shugabar kungiyar Hajiya Saratu Sabo ta yaba wa gwamnan bisa jajircewar sa na ci gaban jihar.

“Mai girma gwamna, kungiyar mu ta gano irin sadaukarwar da kake yi wa jihar mu abin kauna kuma za ta kasance tare da kai a kowane lokaci,” in ji ta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci