OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamna Dikko Radda ya bukaci jami'an tsaro su gaggauta kama wadanda suka kashe jami'in Kwastam

Gwamna Dikko Radda ya bukaci jami'an tsaro su gaggauta kama

Katsina State Governor, Dikko Umar Radda|

Gwamna Dikko Radda ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta cafke wadanda ake kyautata zaton suna da alhakin mutuwar jami’in hukumar kwastam a jihar.

Umarnin ya zo ne a yayin ziyarar ta’aziyya da shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale ya kai wa gwamnan Katsina a ranar Alhamis.

Wasu da ake zargin masu fasa kwauri ne sun kashe wani ma’aikacin hukumar kwastam mai suna Auwal Haruna a wani mummunan hari a shingen binciken Gamji Makaho da ke kan titin Dankama a karamar hukumar Kaita a ranar 17 ga Afrilu.

Gwamnan ya bukaci jami’an tsaron jihar da su bi su damke wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin ganin sun fuskanci hukunci.

Radda ya ce, “Yana da matukar muhimmanci jami’an tsaro da ke da alhakin gudanar da bincike su tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata laifin domin a yi adalci, a madadina da na al’ummar jihar nan, ina jajantawa iyalan Marigayin, da dukkan ma'aikatan kwastam kan asarar da ba za a iya maye gurbinsa ba."

Ya ce, duk da haka, huldar da ke tsakanin kwastam da al’ummomin kan iyaka a jihar na da kyau kuma ya haifar da sakamako mai kyau, don haka akwai bukatar dorewar ta. Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin “saboda ya rasu ne yana kokarin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.”

Tawagar ta kai irin wannan ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin a ranar Larabar da ta gabata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci