OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnan jihar Oyo ya sanya hannu Kan dokar sa ido kan kwangilolin gwamnatin

Gwamnan jihar Oyo ya sanya hannu Kan dokar sa ido kan kwangi

An rattaba hannu kan dokar kafa hukumar sa ido kan kwangilolin gwamnatin a jihar Oyo ta shekarar 2024.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya sanya hannu kan dokar a ranar Alhamis a ofishin gwamnatin dake Ibadan babban birnin jihar.

Yayin da yake bayyana cewa hukumar za ta kasance karkashin jagorancin Babban sakataren sa ido akan ayyuka, Engr. Salawu yayin da Oluwaseun Laurel, zai zama mataimakinsa.

Da yake jawabi, gwamnan ya bayyana cewa sabuwar hukumar za ta yi kokarin ganin an gudanar da ayyukan da suka dace a jihar Oyo.

“Da safiyar yau, na sanya hannu kan dokar hukumar sa ido kan ayyukan jihar Oyo ta shekarar 2024. Mun yi imanin cewa saka idanu kan kwangilar da gwamnati ta bayar wani muhimmin sashi ne na tasarrafi da dukiyar al'umma ta hanyar data dace.

A jawabinsa gwamnan ya godewa ‘yan majalisar dokokin jihar Oyo bisa hadin kan da suke bawa gwamnatinsa domin ganin gwamnatin jihar Oyo ta ci gaba da samar da ayyukan yi.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci