OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kamfanin OICL ya nada Otunba Oriowo a matsayin darakta

Kamfanin OICL ya nada Otunba Oriowo a matsayin darakta

Layiwola Folorunso Oriowo

Kamfanin Odu'a Investment Company Limited ya nada Layiwola Folorunso Oriowo a matsayin Darakta. 

Otunba Oriowo ya maye gurbin Dakta Segun Aina, wanda ya yi nasarar kammala wa’adinsa na shekaru hudu yana jagorantar OICL.

Otunba Oriowo, a cewar Victor Ayetoro, Babban Manajan Sadarwar kamfanin yace, “kwararre ne a harkar sufurin jiragen sama tsawon sama da shekaru 30, wanda ya kammala karatunsa a babbar Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya da ke Zariya, kuma tsohon dalibin Cibiyar horon tukin jirgin sama ta San Carlos dake California a Amurka. Ya halarci horo da dama da suka hada da IATA Training and Development Institute, Montreal, Canada, da United Airline Training School, Denver, Colorado, USA. Ya taba rike mukamin Babban Darakta a Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA), kuma Memba a Hukumar Kula da Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya (NCAT) Zariya da Kamfanin Skyway Aviation Handling Company (SHCOL).

"A halin yanzu shi ne Shugaban Bankin Microfinance na Chanelle, zai kasance tare da sauran Daraktoci wajen tabbatar da cigaban kamfanin OICL.

Otunba Oriowo yana da ƙwarewa a fannoni daban daban saboda haka zai bayar da gudummawa sosai ga ci gaba da aikin farfado da OICL.

Da yake tsokaci game da nadin, Shugaban kungiyar OICL, Bimbo Ashiru ya ce ana sa ran Otunba Oriowo zai kawo dimbin gogewa da kwarewarsa don yin tasiri ga ci gaba da ayyukan kamfanin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci