OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kungiyar Yan awaren IPOB ta gargadi matasa su guji shiga aikin soja

Kungiyar Yan awaren IPOB ta gargadi matasa su guji shiga aik

Kungiyar Yan awaren IPOB, mai fafutukar neman kafa kasar Biafra, ta yi gargadi ga matasa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya su guji shiga aikin soji.

Sakataren yada labarai na kungiyar, Emma Powerful, ya ce zai zama wauta ga duk wani matashin Najeriya ya shiga aikin Soja.

“Matasan kasar Biafra muna horon ku da kar ku shiga aikin daukar ma’aikata a halin yanzu da sojojin Najeriya ke tallata wa,zai zama wauta ga duk wani matashin Najeriya mai hankali, musamman matasan Biafra ya sadaukar da rayuwarsa wajen aikin soja” 

Da take bayyana dalilanta, IPOB ta yi zargin cewa, “’Yan ta’addan da sojoji ke yaka na neman kafa daular Musulunci a Arewa. Wadannan ‘yan ta’adda sun shelanta yaki da gwamnatin Najeriya da sojojinta kuma sun yi nasarar rage karfin sojojin Najeriya. Ga rashin da’a, kabilanci, son zuciya da rashin albashi da ya dabbaibaye rundunar sojojin Najeriya ya tilastawa sojoji da dama yin ritayar gashin kai. Wasu daga cikin sojojin da suka nemi yin ritaya na radin kansu da hukumomin sojin Najeriya suka ki amincewa da su, sun arce a wani abin da rundunar ta kira "Awol". Wadannan abubuwa sun tilastawa Sojojin Najeriya tallata daukar aiki kusan sau biyu ko sau uku a shekara.” 

Sanarwar ta soki sojojin, inda suka yi zargin suna cin zarafin bil'adama musamman 'yan kabilar Igbo.

Matasan yankin Kudu-maso-Gabas sun yi ikirarin cewa sojoji na kai hari tare da tsare mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba. 

Rahoton ya bayar da misalin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan inda kungiyar IPOB ta yi zargin jami’an tsaro sun kashe mutane babu gaira babu dalili. 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci