OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Rage Tallafin Man Fetur

Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Rage Tallafin Man Fetur

Senate Seat

Majalisar dattawa a ranar Larabar ta yi watsi da shawarar kwamitinta na rage kasafin kudin tallafin man fetur a shekarar 2023 daga Naira tiriliyan 3.6 zuwa N1.7trn tare da tabbatar da shirin karbar bashin N8.4 tiriliyan.

 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a ware N3.6 tiriliyan a matsayin tallafin man fetur daga watan Janairu zuwa Yuni na shekara mai zuwa a 2023-2025 a cikin tsarin kasafin kudin da zai gabatar ga Majalissar ranar juma'a mai zuwa.

 Sai dai kwamitocin hadin gwiwa na majalisar dattijai kan kudi da tsare-tsare da harkokin tattalin arziki, wadanda suka yi aiki a kan takardar kasafin sun ba da shawarar cewa a rage kudin tallafin man fetur zuwa N1.7trn a shekarar 2023.

 Majalisar dattijai a cikin shawarwarin ta kuma amince da kara yawan man fetur din da ake haka zuwa ganga miliyan 1.83 a kowace rana.

 Har ila yau, Majalissar ta sahale daidaita farashin chanji kowacce Dala 1 akan naira N437.57.

 Majalisar dattawa ta yarda da karbo sabon rancen Naira Tiriliyan 8.437 daga ciki da wajen kasar nan matukar aka samar da cikakkun bayyanan yanda tsarin karbar bashin zai kasance.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci