OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sanatoci Sun Bukaci Mayar Da Hukumar ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashe Waje Zuwa Ma’aikata

Sanatoci Sun Bukaci Mayar Da Hukumar ‘Yan Najeriya Mazauna

Mambobin kwamitin majalisar dattawa kan kasashen ketare da kungiyoyi masu zaman kansu a jiya Alhamis sun ba da shawarar daukaka hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) zuwa ma’aikatar da ke da cikakken iko.

Sun yi magana ne a lokacin ganawar kwamitin da jami’an NiDCOM, karkashin jagorancin shugabar ta, Abike Dabiri-Erewa a majalisar dokokin kasa, dake Abuja.

 Shugaban kwamitin, Sanata Michael Nnachi, ya ce nauyin da aka dora wa kamfanin na NiDCOM ya fi abin da hukumar za ta iya dauka.

Abike Dabiri ta ce “Akwai bukatar daukaka NIDCOM zuwa cikakkiyar ma’aikatar saboda haka ya kamata sashen shari'a ya fara aiki don sake duba Dokar.

 “Muna rokon Majalisar Dokoki ta kasa da ta taimaka mana domin mu samu ofisoshin nahiyoyi domin mu samu damar shiga kai tsaye ga ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.

 "Rashin samun ofisoshi a kasashen waje ba zai ba mu damar kula da alamuran mutum 10 cikin 100 na 'yan Najeriya mazauna kasashen waje ba."

A nata bangaren Majalisar ta bada tabbacin a shirye take ta bawa hukumar dukkan goyon baya don ganin hukumar ta zama cikakkiyar ma'aikata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci