OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwankwaso Ya Ki Amsa Gayyatar Da Kungiyar Arewa Ta Yi Masa

Kwankwaso Ya Ki Amsa Gayyatar Da Kungiyar Arewa Ta Yi Masa

Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ki amsa gayyatar taron tattaunawa da yan takarar shugaban kasa wanda kwamitin hadin gwiwa na Arewa ta shirya.

 

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, kungiyoyin Arewa da dama ne suka shirya taron tattaunawa wanda suka hada da Arewa Consultative Forum, Arewa House Center for Historical Research, Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation, Northern Elders Forum, Arewa Research and Development Project.

 

Taron dai an shirya shi ne don tattaunawa da 'yan takarar shugaban kasa kan manufofinsu, akidu da tsare-tsarensu akan kasa Najeriya.

 

Yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da wasu jam'iyyu biyu suka halarci gayyatar kungiyar a ranar Asabar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu; da Peter Obi na jam'iyyar Labour da; shi Kwankwaso ana sa ran za su yi ta su tattaunawar ne a ranar Litinin.

 

Sai dai a wata wasika da ya aikewa wadanda suka shirya taron mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Oktoba tare da sa hannun mai magana da yawun sa AbdulMumin Jibrin, ya bayyana cewa lokaci da aka saka don zaman tattaunawa ya zo daidai da jadawalin gangamin yakin neman zabe.

 

Kwankwaso ya kuma kara da cewa matakin da ya dauka na kin amsa gayyatar ya samo asali ne daga wasu bayanai na cewa wadanda suka ki amincewa da takarar shi za su yi amfani da taron wajen marawa wani dan takarar da ya fito da ga Arewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci