OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wani Hadimin Ganduje Ya Zargi Mabiya Kwankwasiyya Da Kai Masa Farmaki

Wani Hadimin Ganduje Ya Zargi Mabiya Kwankwasiyya Da Kai Mas

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya yi zargin cewa wasu ‘yan daba da yake zargin mabiya kungiyar Kwankwasiyya ne a jihar suka kai masa hari.

Kofar Na’isa ya yi zargin cewa maharan sun sace wayar sa ne a yayin da suka daba masa wuka.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a Kofar Dan Agundi.

Kofar Na’isa ya kara da cewa maharan sun kuma tsoratar da masu wucewa lokacin da suka kai masa harin.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya bayyana cewa: “Wataƙila ’yan daban sun yi amfani da damar taron jama’a ne da yin ta’asar su, suna tsoratar da su da kuma suna kwace dukiyoyin su.

“Yan daban sun kai min hari yau a Kofar Dan Agundi inda suka daba min wuka suka tafi da waya ta da ke dauke da layin MTN dina.

“Na yi sa’a cikin yardar Allah ban samu wani mummunan rauni ba amma sun yi nasarar kwace wayata.

"Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da kare rayukan mu daga irin wannan mummunar dabi'a."

Kwankwasiyya kungiya ce ta siyasa domin goyon bayan tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP) gabanin zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

A halin da ake ciki dai har yanzu kungiyar ba ta ce uffan ba kan zargin da aka mata. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci