OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Kwamishiniya Ta Ajiye Mukamin Ta Don Karbar Makamancin Sa A Imo

Kwamishiniya Ta Ajiye Mukamin Ta Don Karbar Makamancin Sa A

Tsohuwar kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara a Zamfara, Haj. Rabi Shinkafi

Kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara a  Zamfara, Hajiya Rabi Shinkafi, ta ajiye mukamin ta domin karbar makamncin mukamin a jihar Imo.

 

Hajiya Shinkafi ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa a yau Alhamis cewa ta ajiye aikin ne domin ta karbi mukamin kwamishiyar a jihar Imo.

 

Tsohuwar kwamishiniyar ta godewa  Gwamna Bello Matawalle da uwargidansa Hajiya A’isha Matawalle bisa bata damar hidimtawa jihar dama kyautata mata.

 

A cewar ta “Duk rade-radin da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta game da murabus na kwata-kwata karya ce; aikin ɓata ne kawai.

 

“Ina da cikakkiyar dangantaka da gwamna da matarsa. Ina daukar su a matsayin dangina kuma suna cikin hoton tafiyata Imo

Ta tabbatar da cewa Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo da Matawalle sun tattauna a matsayin gwamnonin jam'iyyar APC kuma a matsayin abokai kan batun.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci