OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ku Kwantar Da Hankalin ku, Nasara Nanan Tafe - Bwacha

Ku Kwantar Da Hankalin ku, Nasara Nanan Tafe - Bwacha

Sen. Emmanuel Bwacha| Photo Source: Premium Times

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamnan Bwacha ta buƙaci magoya bayanta da sauran jama’a da su kwantar da hankalinsu, bayan soke zaɓen fidda gwani na gwamna na jam'iyar APC a Taraba.

Zaɓen fidda gwanin wanda ya samar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Taraba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da na kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Aaron Arthimas ya fitar a Jalingo.

Sanarwar wacce ta bayyana hukuncin a matsayin koma baya na wucin gadi ta ce Kwamitin yaƙin neman zaben ta sallamar ga duk wani zaɓi da jam’iyyar za ta yanke.

“Ba mu da masaniya kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Jalingo ta yanke na soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Taraba.

“Duk da haka, Muna ƙira ga dukkan masu goyon bayan ƙungiyar mu da su kwantar da hankalinsu domin hakan koma baya ne na wucin gadi.

"Kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan Bwacha tana tabbatar wa kowa da kowa cewa mun yarda da duk wani zaɓi da jam’iyyar za ta yanke.

"Kwamitin zartaswar jam’iyyar na ƙasa ta kasance hukumar da kundin tsarin mulki da dokar zabe suka ba su damar gabatar da ƴan takarar zaɓe a ofisoshi daban-daban.

“A yayin da muke jiran hukuncin majalisar na jam’iyyar, ƙungiyar lauyoyin mu za ta yi nazari kan hukuncin bayan karbar kwafin kafin yanke hukunci kan mataki na gaba,” in ji sanarwar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sanarwar tace majalisar har yanzu ba ta damu da wannan hukunci na wucin gadi da kotun matakin farko ta yanke ba tare da shawartar duk kodinetoci da magoya bayansu da su ƙara kaimi wajen yaƙin neman zaɓe.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci