OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Kotu Ta Umarci A Biya El-Rufa'i N10m Kan Batanci

Kotu Ta Umarci A Biya El-Rufa'i N10m Kan Batanci

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta umurci kamfanin buga jaridun nan na Today Publishing, mawallafin jaridar The Union, da ya bayar da hakuri tare da biyan Naira miliyan 10 bisa zargin bata sunan Gwamna Nasir El-Rufa'i.

Gwamna El-Rufai ya kai karar kotu ne a shekarar 2015 bayan jaridar ta buga labarin bayyana kadarorin sa, wanda gwamnan yace labarin karya ne.

Justice M.L. Muhammed na babbar kotun jihar Kaduna wanda ya yanke hukuncin, ya umarci wadanda ake kara da su biya El-Rufa'i kudi naira miliyan 10 a matsayin diyya kana su bayar da hakuri wanda dole ne a buga a manyan jaridun kasa.

Kotu ta kuma haramta wa wadanda ake tuhuma ci gaba da bata sunan Gwamnan.

Idan zaku tuna, an buga labari ne a shafin farko na jaridar The Union a ranar 2 ga watan Yulin 2015, wanda ya ce gwamnan ya bayyana kadarorin da ya kai N90bn da kuma gidaje 40.

Lauyan El-Rufai, A.U. Mustapha, SAN, ya yaba da hukuncin. 

A nasa bangaren, gwamnan ya yi maraba da hukuncin inda yace "'yancin wallafawa ba lasisi ba ne na bata sunan mutane ko sanya jita-jita da zage-zage a matsayin aikin jarida".

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci