OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

El-Rufa'i Ya Kori Malamai 233 Inda 12,254 Ke Shirin Zana Jarabawar Kwarewa

El-Rufa'i Ya Kori Malamai 233 Inda 12,254 Ke Shirin Zana Jar

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Gwamna jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya sallami malamai 233 daga aiki saboda gabatar da satifiket na bogi yayin daukan su aiki.

Hakan yazo ne cikin bayyanin shugaban hukumar kula da ilimi na SUBEB a jihar, Tijjani Abdullahi a ranar Alhamis.

Abdullahi yace an sallami malaman ne sakamokon bincike da aka gudanar akan su wanda ya nuna cewa suna amfani da takardun bogi.

Shugaban SUBEB din ya kara da cewa binciken ya fara ne daga watan Afrilun shekarar 2021.

Yace hakan yunkuri ne na hukumar don tabbatar da ingancin malamai a jihar.

A cewar sa takardu 451 suka samu tantancewa daga makarantu 13 wanda 9 daga ciki suka amsa.

Haka kuma, hukumar zata gudanar da sabon jarrabawar cancanta ga malamai 12,254 daga watan Janairun 2022.

 

Shugaban hukumar ya kara da cewa hakan wani kokari ne na inganta ilimi da masu bayarwa a jihar Kaduna.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci