OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnatin Kaduna Za Ta Biya Ma'aikata Alawus Din Karshen Shekara

Gwamnatin Kaduna Za Ta Biya Ma'aikata Alawus Din Karshen She

Gwamna Nasir El Rufa'i

Gwamnan Kaduna Nasir El Rufa’I ya amince da biyan ma’aikatan jihar kudin alawus din karshen shekara naira miliyan dubu da dari uku da tamanin da biyu.

Mai ba gwamnan shawara kan yada labarai, Muyiwa Adekeye ya bayyana haka a sanarwar da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na kasa.

Sanarwar ta ce dukkan manyan ma’aikatan gwamnati za su samu alawus na kashi talatin a albashin su, su kuma kananan ma’aikata za su karbi kashi dari na alawus din nasu a wannan wata.

Ya ce gwamnatin za ta bayar da kudin ne domin karfafawa ma’aikatan ta gwiwa da kuma tabbatar da walwalar su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci