OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kano: Sarkin Tsaftar Hausawan Afrika Ya Danganta Ambaliyar Ruwan Bana Da Cin Hanci Da Rashawa

Kano: Sarkin Tsaftar Hausawan Afrika Ya Danganta  Ambaliyar

Ambaliyar ta jawo asarar dukiya da rayukan jama'a a bana

Sarkin tsaftar Hausawan Afrika kuma shugaban makarantar kula da lafiya da tsaftar muhalli ta jihar Kano, Dr. Bala Getso ya alakanta yawan ambaliyar ruwan da ake samu a damunar bana da cin hanci da rashawa, da ya janyo ake yin gine-gine ba bisa ka’ida ba.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro kan ranar muhalli ta duniya, da ya gudana a dakin taro na Coronation Hall da ke fadar gwamnatin Kano.

Yace halayen dan adam ne ke haddasa matsalolin da muhalli ke fuskanta, wanda magance su ne zai takaita cutukan dake da alaka da muhalli.

Da yake jawabi, kwamishinan muhalli na jihar Kano wanda Abba Adamu Takai ya wakilta, yace duk ba zasu iya sama faruwar ambaliyar ruwan ba, amma sun yi iya kokarinsu wajen takaita faruwarsa a nan Kano.

Kwamishinan muhallin ya kuma ce a kullum suna aikin kwashe shara don tsaftace jihar Kano.

Ambaliyar ruwan bana ta yi mummunan lahani ga jihohi daban daban, inda aka samu wasu yankunan da gine-gine akan hanyoyin da ruwa ke wucewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci