OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jariri Guda Na Rasuwa A Cikin Kowane Minti 15 Sakamakon Cutar Tetanus —UNICEF

Jariri Guda Na Rasuwa A Cikin Kowane Minti 15 Sakamakon Cuta

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce bayanai sun nuna cewa jariri daya na mutuwa sakamakon cutar tetanus a duk minti goma sha biyar.

Shugabar tawagar canjin halayyar al’umma ta UNICEF a jihar Taraba, Jennifer Dabo, ta bayyana hakan a yau Lahadi a wani taron wayar da kan ‘yan jarida kan yaki da Tetanus a jikin yara da mata masu juna biyu, MNTE, a jihar Taraba.

Ta ce akasarin lokuta kafafen yada labarai basu cika yada bayanai game da cutar tetanus ta jarirai ba duk da tana daya daga cikin cututtuka shida masu kashe jarirai a Najeriya.

Ta kuma bayyana matsalolin al’adu, rashin tsaro, rashin tsafta da masu kula da haihuwa na gargajiya ke yi da dai sauransu a matsayin dalilan da suka haifar da yaduwar cutar ta MNT a Arewacin Najeriya.

Har ila yau, ta ce Najeriya na cikin kasashen da Tetanus na yara da mata masu ciki (MNT) ke damun lafiyar al'umma har yanzu ba a kawar da su ba.

 Malamar kiwon lafiya karakashin hukumar kula da kiwon lafiya matakin farko ta jihar Taraba, TSPHCDA, Mercy Maigoge, ta ce suna mayar da hankali kan kananan hukumomi hudu a jihar da allurar rigakafin cutar tayi karanci, wadanda suka haɗa da kananan hukumomin Bali, Wukari, Yorro da Kurmi.

Maigoge ta bayyana cewa  Sashin Al'ummar da suka maida hankali wajen yiwa allurar rigakafin tetanus din tare da tallafin UNICEF mata ne masu shekaru tsakanin 15 zuwa 49.

Ta kuma tuni suka tura kwararrun ma’aikata don gudanar da alluran rigakafin a fadin kananan hukumomin hudu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci