OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jam'iyyar PDP A Jihar Zamfara Ta Saka Ranar Da Za'ayi Zaɓen Fidda Gwani

Jam'iyyar PDP A Jihar Zamfara Ta Saka Ranar Da Za'ayi Zaɓen

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Zamfara ta sanya rana domin sake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a jihar.

Jam'iyar ta saka gobe juma'a a matsayin ranan zaɓen, biyo bayan hukuncin kotu.

Idan za'a iya tunawa a makon da ya gabata wata babbar kotun tarayya a jihar ta soke zaɓen fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar da Alhaji Dauda Lawal Dare ya lashe.

A cewar kotun zaɓen ya saɓawa saɓa ƙa’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, cewar Jaridar Daily Trust.

Shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Ahmad Sani Kaura, ya ce ana shirye-shiryen gudanar da zaɓen  a jihar cikin kwanciyar hankali, inda ya ƙara da cewa za a samar da daidaito ga duk wanda ya tsaya takara.

“Jam’iyyar PDP ta kasance mai bin doka da oda kuma muna bin umarnin kotu na gudanar da sabon zaben fidda gwani.  

"Waɗanda suka fafata sune zasu sake karawa wato Alhaji Dauda Lawal Dare, Ibrahim Shehu Gusau, Wadatau Madawaki da Hafiz Nuhuche.

“Hedikwatar jam’iyyarmu ta ƙasa ta tsara sake gudanar da zaben a ranar 23 ga Satumba 2022, inda Jami’ai daga hedikwatar Gusau zasu zo domin gudanar da zaɓe cikin lumana da karbuwa.

“Kamar yadda nake magana da ku, ana gudanar da ‘yan majalisu a unguwanni don tabbatar da bin doka da oda saboda wani ɓangare na abin da kotu ta ce an cire mata daga cikin jerin wakilai.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci