OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ina Jin Takaicin Yajin Aikin ASUU— Buhari

Ina Jin Takaicin Yajin Aikin ASUU— Buhari

Muhammadu Buhari

Shugaban Ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sake yin ƙira ga ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU da ke yajin aiki da su koma ajujuwa tare da ba su tabbacin magance matsalolin da suke fama da su.

Buhari yayi wannan  jawabi ne a yau Asabar a Abuja, a yayin bikin cikar Najeriya shekaru 62 da samun ƴanci.

Shugaban ya ce yana jin takaicin yadda ilimi ke ƙara tabarbarewar a manyan makarantun ƙasar nan.

A cewarsa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada-hadar albarkatun ƙasa da ƙasa da kuma na ƙasa baki daya, wajen samar da tallafin ilimi.

“Dole ne in furta cewa ina jin zafi sosai game da matsalar da ake fama da ita a tsarin karatunmu na manyan makarantu.

“Ina amfani da wannan bukin ranar samun ƴancin kai ne domin nanata ƙirana ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aikin da su dawo ajujuwa.

"Ina kuma basu tabbacin shawo kan matsalolin da suke fuskanta ta hanyar ƙarancin kayan aiki.

“Wannan gwamnatin ta samu ci gaba mai inganci wajen gyara waɗannan al’amura da aka kwashe sama da shekaru goma sha daya ana yi,” in ji shi.

A cewarsa, hakan ya biyo bayan yadda ilimi ke kan gaba wajen tabbatar da ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

“Kamar yadda muka samar da dukkan matakan tabbatar da cewa Najeriya ta samu matsayinta a cikin ƙungiyar kasashen duniya.

"Mun fahimci mahimmancin jama’a masu ilimi a matsayin maganin mafi yawan ƙalubalen da muke fuskanta", cewar Jaridar Daily Nigerian.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci