OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jami'ar Abuja zata cigaba da aiki duk da yajin aikin da ASUU keyi

Jami'ar Abuja zata cigaba da aiki duk da yajin aikin da ASUU

Jami’ar Abuja, ta yi watsi da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU reshen jami’ar ta shiga.

 

A wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a shugaban jami’ar, Farfesa Abdul-Rasheed Na’Allah ya bayyana cewa jami’ar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda aka saba, ciki har da jarabawar da ake yi da kuma taron majalisar zartarwar jami'ar.

 

VC din ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da Provost, Deans, Daraktoci, da shugabannin sassan ilimi kamar yadda mukaddashin Daraktan hulda da jama’a, Dakta Habib Yakoob, ya bayyana a ranar Juma’a. 

 

An ruwaito VC na cewa,"wannan jami’a ba ta yajin aiki, wasu sun ce sun ayyana yajin aiki, amma dukkan mu tare da mahukunta mun yanke shawarar cewa ayyukanmu na yau da kullum a jami’ar zasu ci gaba. ”

 

 Farfesa Abdulrashid ya kuma bayyana yajin aikin a matsayin wata hanyar kawo rudani da rabuwar kai a alamuran jami'ar.

 

Yayin da hukumar jami'ar ta dage kan ci gaba da karatu, har yanzu ba a san adadin malaman da zasuyi mata biyayya ba.

 

Har yanzu dai kungiyar ASUU ta kasa ba ta ce uffan ba kan halin da ake ciki a UniAbuja.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci