OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NAFDAC Ta Ɗauki Matakan Daƙile Masu Rarraba Gurɓatattun Magungunan Gargajiya

Hukumar NAFDAC Ta Ɗauki Matakan Daƙile Masu Rarraba Gurɓa

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, (NAFDAC) a karshen mako ta fara daukar matakin dakile duk wasu masana'antun da masu rarraba kayan ganyen da ke dauke da tarin taba, hodar iblis da tabar wiwi.

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna wani yanayi mai hatsarin gaske wajen amfani da irin wadannan abubuwa masu dauke da tarin tabar tabar wiwi a wasu lokutan a tsakanin ‘yan Najeriya daga kowane jinsi.

Sa'annan musamman masu sana’a, direbobi, masu matuƙa babura da sauransu, cewar Jaridar Vanguard.

Da take yi wa manema labarai karin haske game da haramtattun kayan maye da aka fi sani da akurkura, da sauran kayan maye a kasar nan, Darakta Janar na Hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ya ce akurkura da sauran ganye da suka hada da magungunan kara sha'awa da aka yi da wiwi, na kawo rashin lafiya har ma da rasa rai.

Adeyeye ta bayyana cewa ana amfani da wadannan sinadarai za su iya yin illa ga gabobin jiki kamar su kwakwalwa, koda da hanta.

Ta ce suna kuma iya sauyawa ɗan Adam tunani ya shiga halaye marasa kyau kamar sace-sace da kisa.

Shugabar ta jaddada cewa hukumar ta za ta sanya kafar wando Guda da duk masu irin wannan haramtacciyar sana'a.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci