OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mazauna Unguwar Mararaba A Nasarawa Sun Koka Bisa Karuwar Kudin Wutar Lantarki

Mazauna Unguwar Mararaba A Nasarawa Sun Koka Bisa Karuwar  K

Mazauna garin Mararaba da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa sunyi barazanar yin zanga-zanga kan kudin wutar lantarkin da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya yi.

 A wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, Mazauna yankin sun bayyana cewa kiyasin kudaden da aka raba na watannin Agusta da Satumba sun nuna an samu karin kudin wutar.

Richard Ekoja, da yake kasuwanci a Mararaba, ya ce kamfanin wutar sun Bukaci ya biya naira 22,269.70 a watannin Agusta da Satumba sabanin N6,000 da N9,000 Daya saba biya a watannin baya.

 “babu wani dalili da zai sa AEDC ta fito da wannan kudiri a daidai wannan lokaci da ‘yan Najeriya ke kokawa da tabarbarewar tattalin arziki" a cewar Ekoja.

 Ekoja wanda ya caccaki Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) kan dakatar da na'urar meter da ake amfani da ita a baya ya ce ya kamata kamfanin ya samar da na'urar tantance adadin wutar lantarki da mutum yake amfani da shi kafin ta yanke wannan hukunci.

 Leonard Ogwuche, wanda shi ma mazaunin Mararaba ne, ya ce AEDC na fakewa da kiyasin kudin wutar suna cin zarafin kwastomomi.

Ya ce a kodayaushe masu amfani da wutar lantarki a yankin suna ba da gudummawar kudi domin gyara taransfoma a lokacin data samu matsala da sauran kananan gyare-gyare ba tare da kamfanin wutar ya biya su ko sisi ba. 

 “Duk lokacin da muka kai rahoton wata matsala ga AEDC, za su gaya mana mu rubuta kuma idan muka rubuta za su dauki lokaci basu magance matsalar ba" a cewar mista Leaonard.

 NAN ta ruwaito cewa wani jami’in kamfanin daya bukaci a sakaye sunan sa ya ce sabon kudin harajin ya zo kenan domin kamfanin na biyan makudan kudade domin sayen wutar lantarkin da zai rarrabawa kwastomomi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci