OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar Kare Aukuwar Hadura Ta Kasa Ta Samu Sabbin Motocin Sintiri 316

Hukumar Kare Aukuwar Hadura Ta Kasa Ta Samu Sabbin Motocin S

Gwamnatin tarayya ta bawa hukumar kare aukuwar hadura ta kasa, FRSC sabbin motoci, dari uku da goma sha shida domin bukasa ayyukan su a manya tituna dake fadin kasar nan.  

A ta bakin babban Sakataren gwamnati, Boss Mustapha wanda ya kaddamar da amfani da motocin, yace gwamnatin ta bawa hukumar sabbin baburan ne don karfafa ayyukan ta na kare ababen raya kasa da gwamnati ta shimfida a fadin kasar nan.

"Gwamnati ta kuduri aniyyar samarwa da hukumomi kayan aiki da suke bukata don tafiyar da ayyukan su tare da fatan hakan ya tabbata, la'akkari da kokarin gwamnatin shugaban kasa,  Muhammadu Buhari na samar da ayyukan raya kasa.

"An samar da sabbin motocin sintiri ga hukumar ta kare aukuwar hadura, domin tabbatar da ayyukan ta na kare yawan faruwar haddura a kasa tare da lafiyar hanyoyin sufuri da gwamnati ta tana da a fadin kasa. 

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ya rawaito, mukaddashin shugaban hukumar kare aukuwar hadura ta kasa, Dauda Biu ya jaddada cewa hukumar ta samu kwarin gwiwa wajen kara bunkasa ayyukan ta a fadin Najeriya, tare da yin alkwarin raba motocin ga rassan hukumar dake fadin kasar nan ba tare da son zuciya ba.

 

Source: Daily Nigerian

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci