OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Mota ta murkushe wani mutumi har lahira a jihar Ogun

Mota ta murkushe wani mutumi har lahira a jihar Ogun

Mota ta murkushe wani mutumi har lahira a hanyar kauyen Lenuwa da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan. 

 

Hatsarin ya afku ne a ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 9:55 na safe lokacin da wata mota kirar Mitsubishi mai lamba KTU209YF ta kwace wa direban ta kuma afka Kan mutumin dake tafiya a kafa a gefen titin.

 

Wani ganau mai suna Moses ya bayyana yanda lamarin ya faru “Motar na tsananin gudu akan titin da zai kaika Ibadan kwatsam sai ta kwace ta afka wa mutumin da ke bakin titi ta jefa mutumin cikin wani rami da ke kan babbar hanyar"

"Direban da yaron motar sun samu raunuka saboda motar sai data juya sau biyu kafin ta yi taho-mu-gama da mutumin. Tuni an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji Moses.

 

Jami’ar hulda da jama’a ta jihar, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin, Inda tace likitoci sun tabbatar da mutuwar mutumin da motar ta murkushe.

 

"Direban ya taho ne daga Legas, ya nufi kauyen Lenuwa da ke kan hanyar Ibadan. Rahotanni sun tabbatar da gudun wuce sa'ar da direban keyi ne yayi sanadin wannan hatsarin da ya jawo asarar rai"

 "An garzaya da direban, yaron motar da mutumin da hatsarin ya rutsa da su asibiti a Sagamu domin yi musu magani Inda anan likitan daya duba lafiyar su ya tabbatar da mutuwar mutumin jim kadan bayan isar sa asibiti. An dauko gawar an ajiye ta a dakin ajiye gawa na asibitin Idera.” a cewar Omolola.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci