OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kwamishinan ilimi ya zagaya cibiyoyin jarabawar JAMB a Oyo

Kwamishinan ilimi ya zagaya cibiyoyin jarabawar JAMB  a Oyo

Kwamishinan Ilimi na Jihar Oyo, Farfesa Salihu Adelabu ya jagoranci tawagar duba yadda ake gudanar da jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire da ake gudanarwa a babban birnin Ibadan ranar Juma’a.

 

 Wasu cibiyoyi da tawagar ta duba sun hada da Cibiyar Ilimi ta Kwalejin Yimbo, Jami'ar Ibadan, Cibiyar Koyon nesa, Cibiyar ICT, da Esther Oshikoya CBT da dai sauransu.

 

Da yake jawabi yayin atisayen, Farfesa Salihu ya bayyana jin dadinsa da yadda ake gudanar da jarabawar a cibiyoyin, inda ya yabawa hukumar ta JAMB bisa gudanar da jarrabawar ba tare da cikas ba.

 

Ya ci gaba da cewa gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Gwamna Seyi Maknde za ta ci gaba da samar da yanayin da zai sa harkar ilimi ta bunkasa a jihar. 

 

Ya yi kira ga masu cibiyoyin jarabawar da suyi kokarin yin rajista da ma'aikatar ilimin jihar.

 

Kwamishinan ya kuma bukaci cibiyoyin da suke da burin cigaba da koyar da karatu bayan kammala jarabawar da su yi rajista da ma’aikatar ilimi mai zurfi sukuma cika dukkan ka’idojin da aka gindaya ciki har da biyan kudaden gudanarwa ga ma'aikatar ilimi.

 

Tawagar sa idon ta hada da Daraktan Gudanarwa Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha, Christiana Bolaji, da sauran Daraktocin Ma’aikatar.

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci