OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan jarida sun bukaci a gyara dokar tsaron intanet

Yan jarida sun bukaci a gyara dokar tsaron intanet

Wata yar jarida Rafat Salami,ta bukaci gwamnatin Tarayya tayi gyara ga dokar tsaron intranet domin tabbatar da Yan jarida zasu iya gudanar da aikin su ba tare da wani shinge ba a yayin wani horo a Ilorin.

 

Salami itace mataimakiyar darakta a gidan rediyon Muryar Najeriya VON a Abuja, ta jaddada bukatar a samu sauye-sauye a yayin wani horo na kwanaki uku kan kare lafiyar jinsi, inda ta bayyana cewa tanade-tanaden da ke cikin dokar na kawo cikas ga aikin jarida. 

 

“Yawancin ’yan jarida ba su san abin da ke cikin Dokar Laifukan Intanet ba.Don haka a matsayinmu na ’yan jarida, ya kamata mu nemi gyara domin wannan doka taci karo da aikin da kundin tsaron mulkin kasa ya daura a wuyan Yan jarida"

 

Salami, wacce tana daya daga cikin masu horaswa a shirin horaswar tace “tunda muna da haƙƙin da za a mutunta mu, muna kuma da alhakin da ya rataya a wuyanmu ya kamata a kara wayar dakan mutane game da batun cin zarafi a wuraren aiki don tabbatar da mutunta mata a wurin aiki," in ji tsohon sakataren kungiyar 'yan jarida ta Najeriya, FCT Council.

 

 Salami ta kuma bukaci kungiyar ta NUJ da ta tabbatar da wakilci a kwamitin korafe-korafen wuraren aiki tare da gudanar da bita kan kare kai da karfafawa mata gwiwa wajen kai rahoton cin zarafi.

 

Ta kuma bukaci mahalarta taron da su tabbatar da tsaro wajen gudanar da ayyukansu, inda ta kara da cewa “duk girman labari bai kai ka sanya rayuwar ka a hadari ba " 

 

Salami ta bukace su da su kasance cikin shiri a kodayaushe don fuskantar lamurra na gaggawa saboda za su iya tasowa a kowane lokaci.

 

 Kungiyar ‘yan jarida mata ta Najeriya, NAWOJ, tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan jarida ta Norway, Norsk Journalist lag, ne suka shirya horon wadda ta hada da mahalarta 30 wadanda suka kunshi mata 25 da maza biyar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci