OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

"Hauhawar farashi zai ragu da kaso 23 a 2025"- IMF

Asusun bada lamuni na duniya yayi hasasshen hauhawar farashin da ake fama dashi a kasar nan zai ragu da kaso 23 a shekarar 2025.

 

Hasashen na IMF na kunshe a wata sanarwa da asusun ya fitar yayin taron yin duba kan tattalin arzikin kasashen duniya Hadin gwiwwa da bankin duniya da aka gudanar a birnin Washington D.C, a ranar Talata. 

 

Daniel Leigh, Shugaban Sashen Bincike na IMF, ya bayyana tasirin sauye-sauyen matakan tattalin arzikin Najeriya, da suka hada da daidaita farashin canji, wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki zuwa kashi 33.2 cikin 100 a watan Maris. 

 

Idan za'a iya tunawa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.2. bisa ga bayanan baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar.

 

Haka zalika, hauhawar farashin kayan abinci ya karu zuwa sama da kashi 40 cikin dari a rubu'in farko na shekarar 2024.

 

 Leigh ya ce, "Munyi hasasshen hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 23 cikin 100 a shekara mai zuwa sannan ya dada raguwa da kashi 18 cikin 100 a shekarar 2026." 

 

Ya kuma yi karin haske kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya da ake sa ran zai tashi daga kashi 2.9 da aka samu a bara zuwa kashi 3.3 cikin 100 a bana. Inda ya danganta hakan da farfadowar da ake samu a fannin man fetur, da inganta tsaro, da kuma ci gaba a fannin noma.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci