OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Najeriya Da Masar Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwanci Ta dala Miliyan 30

Najeriya Da Masar Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwan

A wani yunkuri na karfafa alaka tsakanin Najeriya da Masar, kungiyoyin kasuwanci a kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa na dala miliyan 30.

 

 An rattaba hannu kan hadin gwiwar ne a taron kasuwanci da baje koli na Najeriya da Masar (NETCE) irinsa na farko da aka kammala a birnin Alkahira dake Masar.

 

 Shugaban kungiyar ‘yan kasuwan Afirka ta Masar (EABA), Dr Yousrey El Sharkawi da Mr Mahmood Ahmadu, shugaban kungiyar hadin kan al’adun gargajiya da zamantakewar tattalin arzikin kasar Masar (NESCEF), ne suka bayyana hakan a karshen taron na kwanaki uku, wanda kungiyoyin tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Alkahira suka shirya.

 

 A wata sanarwa da Abdul-Razaq Musa, babban mataimakin shugaban NESCEF, ya fitar a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa kamfanoni shida daga kasashen biyu sun amince da yin hadin gwiwa a bangarorin gine-gine, da kayan aikin likitanci, da noma, da ma'adinai hadi da fasahar kerekere.

 

Ya kuma yaba wa kamfanoni masu zaman kansu na kasashen biyu bisa daukar kwararan matakai don aiwatar da hadin gwiwar domin bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.

 

 Karamin ministan ayyuka da gidaje na Najeriya, Ibrahim El-Yakub, wanda ya halarci taron, kuma ya zagaya wasu rukunin gidaje da kamfanoni masu zaman kansu suka gina a kasar Masar, ya bayyana aniyar Najeriya na hada kai da Masar a fannin gidaje domin a kowacce Shekara akalla akan bukaci gidaje 200,000 a kasar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci