OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hatsarin Kwalekwale Ya Jawo Asarar Rayuka Biyar A Jigawa

Hatsarin Kwalekwale Ya Jawo Asarar Rayuka Biyar A Jigawa

Akalla mutane biyar ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.

Ku tuna cewa an samu labarin mutuwar wasu matasa biyu kimanin mako guda da ta gabata a karamar hukumar Miga.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Adam, ya ce mutanen biyar da suka mutu, sun mutu ne a yayin da suke dawowa daga sallar Jumma’a a lokacin da hatsarin ya afku.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Adam ya ce: “Mutane biyar ne suka mutu, an ceto hudu a wani hatsarin kwale-kwale a kauyen Martaba da ke karamar hukumar Gwaram."

Ya kuma bayyana cewa: “A ranar Jumma’a, 2 ga watan Satumba, 2022, da misalin karfe 7:00 na dare, an samu rahoton kifewar wani kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji tara (9)."

A cewar sa, an ceto mutane hudu yayin da aka gano gawarwaki biyar cikin ruwan. 

Adam ya kara da cewa tare da taimakon 'yan gari aka samo gawarwakin biyar. 

 Yayin da aka mika gawarwakin ga iyalan su, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Tafida ya jajanta wa iyalai da ‘yan uwan ​​mamatan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci