OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane 30 Sun Bata Sanadiyar Kifewar Jirgin Ruwa A Anambra

Mutane 30 Sun Bata Sanadiyar  Kifewar Jirgin Ruwa A Anambra

Kimanin mutane 30 ne ake zargin sun bata yayin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji 85 ya kife a garin Umunnankwo da ke karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.

 

Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Juma'ar data gabata.

 

 A cewar wani ganau, kwale-kwalen ya taso ne daga gadar Onukwu inda ya nufi kasuwannin Nkwo da Ogbakuba; duka a karamar hukumar Ogbaru, lokacin da ya kife.

 

 Shaidan gani da ido ya ce kawo yanzu ba'a gano mutane 30 ba daga cikin wadanda suka fada ruwan.

 

 Da yake tsokaci kan lamarin, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Ogbaru, Hon. Pascal Aniegbuna, ya ce an ceto wasu daga cikin fasinjojin yayin da wasu da dama suka rasa rayukansu.

 

 A halin yanzu, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ogbaru ta tarayya, Hon. Victor Afam Ogene, ya bayyana alhininsa game da hatsarin.

 

 Ogene, wanda shi ne dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Ogbaru a karkashin jam’iyyar Labour a 2023, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya ce ya kadu matuka dangane da mummunan hadarin jirgin ruwa da ya yi sanadin salwantar rayukan mutanen da dama.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci