OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwale-kwale dauke da fasinjoji 50 ya kife, mutane 33 sun bata a Jihar Neja

Kwale-kwale dauke da fasinjoji 50 ya kife, mutane 33 sun bat

Wani Kwale-kwale dauke da fasinjoji hamsin (50) ya kife a kogin Kaduna na jihar Neja yayin da wasu mutane 33 suka bata. 

Kamar yadda muka samu, Kwale-kwalen ya kife ne a daren jiya (Juma’a) a tsakanin kauyen Danchitagi da ke karamar hukumar Lavun da Gbara a karamar hukumar Mokwa a jihar.

Kwale-kwalen ya dauki fasinjojin ne da ke dawowa daga kasuwar Danchitagi na mako-mako da kuma wasu da ke dawowa daga bikin aure daga kauyukan da suke makwabtaka.

Daily Trust ta ruwaito cewa an ceto fasinjoji goma sha bakwai yayin da wasu kuma ba a gan su ba.

Wani mai kwarewa a kan ruwa a yankin da ya zanta da Jaridar ya ce: “A yanzu, cikin fasinjoji sama da 50 da ke cikin wannan kwale-kwalen, mutane 17 ne kawai aka ceto da ran su.

“Mun yi imanin sauran ba su da rai saboda sun shafe sa’o’i da dama a cikin ruwa.

“Haka zalika ruwan ya yi yawa a yanzu saboda ruwan sama.

“Har yanzu muna yin iya kokarin mu wajen neman sauran mutanen.

"Amma baza a iya tabbatar da samun masu rai ba."

A halin da ake ciki babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja (SEMA), Ahmed Ibrahim Inga ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa tuni hukumar ta kaddamar da aikin ceto.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci