OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hatsarin Kwale-Kwale a Jigawa: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa Bakwai – ‘Yan Sanda

Hatsarin Kwale-Kwale a Jigawa: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya K

Boat Mishap

Biyo bayan wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a ranar Lahadi, adadin wadanda suka mutu ya kai bakwai.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a wata sanarwa da ta fitar ta ce kwale-kwalen da ke jigilar mutane 13 ya bugi wani abu kuma ya kife.

Wani likita a babban asibitin Ringim ne ya tabbatar da mutuwar mutane biyu.

Sanarwar wacce mai magana da yawun rundunar, Lawan Shiisu ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, ‘yan sanda tare da wasu 'yan garin sun sake gano wasu gawarwaki biyar.

A cewar Shiisu, "Rahoton ya nuna cewa an sake gano wasu gawarwaki biyar yayin da mutum daya ya bace," daga hatsarin kwalekwalen.

Ya bayyana cewa rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin ne kuma ta fara aiki tare da 'yan garin wanda ya kai ga fito da mutane bakwai.

A halin da ake ciki biyu daga cikin bakwai din da aka bayyana sunayen su Bara’atu Garba mai shekaru 30, da Mahmud Surajo mai shekaru 3 sun rasu a asibiti.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, ana ci gaba da aikin ceton sauran mutanen.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci