OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Harin Jirgin Kasa: Buhari Ya Yabawa Gwamnatin Sa Kan Kubutar Da Sauran Wadanda Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Harin Jirgin Kasa: Buhari Ya Yabawa Gwamnatin Sa Kan Kubutar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa gwamnatinsa kan ganin an sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su watanni shida da suka gabata a wani jirgin kasa mallakin gwamnati.

Gwamnatin kasar ta sanar a ranar Laraba cewa an sako sauran mutane 23 da aka yi garkuwa da su da misalin karfe 4 na yamma.

Suna daga cikin dimbin mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

Jirgin dai ya taso ne daga Abuja zuwa Kaduna inda 'yan ta’adda su ka kai masa hari aKaduna.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar, Mista Buhari "ya yabawa gwamnatinsa kan yadda ta magance matsalar rashin tsaro tare da dakile ayyukan ta'addanci, 'yan fashi da garkuwa da mutane da ake yi a baya-bayan nan, inda ya ba da tabbacin cewa za a yi kokarin kawo karshen matsalar."

Shugaban ya bayyana farin cikinsa da jin dadinsa ga sojoji da ma sauran jami’an tsaro na ganin an sako sauran fasinjoji 23 da suka rage.

“Al’ummar kasar na mika godiyar ta ga rundunar soji da sauran jami’an tsaro da na leken asiri kan nasarar da aka samu wajen gudanar da aikin da aka yi wanda ya kai ga sako mutanen da aka yi garkuwa da su,” Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ya rubuta a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai.

Ya tabbatar da cewa hukumomin sun yi matukar kokarin da dole a yaba musu.

“Rundunar sojojin kasar nan suna da kokari sosai.

Idan aka ba da goyon baya da ƙarfafawa kamar yadda muke yi, babu wani aiki da ba za su iya cim ma ba.

"Na yaba musu bisa wannan gagarumin kokari, in ji Mista Shehu.

Yayin da yake nuna jin dadinsa da sakin sauran mutanen da aka yi garkuwa da su, Mista Buhari ya kuma taya iyalan wadanda lamarin ya shafa murnar dawowar 'yan uwan su cikin koshin lafiya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci